ABNA24 : Ma'aikatar makamashin kasar ba ta bayyana wanda ke da hannu a harin ba.
Saidai a wata sanarwa da Saudiyyar ta fitar, wacce kamfanin dilancin labaren kasar na Saudi Press Agency, ya nakalto, ta yi tir da harin, wanda ta ce an kai shi ne kan Saudiyya da tattalin arzikin duniya wanda babban nakaso ne ga samar da makamashi a duniya.
Babu dai rahoton samun hasarar rai a gobarar data tashi bayan harin.
Duk da cewa Saudiyya bata bayyana wanda ta ke zato da kai mata harin, sanin kowa ne Saudiyya na fuskantar hare haren ramuwar gayya daga Yemen, sakamakon yakin da taka jagoranta kan kasar na tsawon shekaru shida.
A ranar Litini data gabata dai Saudiyya, ta sanar cewa a shirye take ta tsagaita a yakin a shiga tsakanin MDD, saidai ‘yan kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen din da aka fi sani da ‘yan houtsis, sun yi fatali da tayin na Saudiyya, wanda suka ce babu wani sabon abu da za’a girba a ciki.
342/